9 Yuni 2026 - 08:58
Source: ABNA24
Sojojin Amurka Sun Taimaki Isra’ila Wajen Dakile Makamai Masu Linzami Na Iran

Wani jami'in Amurka wanda ya gwammace a sakaya sunansa da asalinsa, ya ce: "Mun harba makamai masu linzami na dakile hari a lokacin arangama ta baya-bayan nan tsakanin Iran da Isra'ila".

Kamfanin Dillancin Labaran Ƙasa Da Ƙasa Na Ahlul-Baiti (As) – Abna - ya bayar da rahoton cewa: Wani jami'in Amurka ya bayyana a jiya Litinin cewa an harba makamai masu linzami na dakile hari a lokacin arangama ta baya-bayan nan tsakanin Iran da Isra'ila.

Jami'in Amurka wanda ya gwammace a sakaya sunansa da asalinsa, ya ce: "Mun harba makamai masu linzami na dakile hari a lokacin arangama ta baya-bayan nan tsakanin Iran da Isra'ila”.

Ya kara da cewa: "Muna ci gaba da kimanta irin makaman da sojojinmu suka dakile da kuma wanda ke da alhakin harba su”.

Sojojin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun kai hare-hare a kan wurare a cikin Isra’ila Azzaluma, a matsayin ramuwa ga cin zarafi da ta ke yi a yankin kudancin birnin Beirut na Lebanon tun daga daren jiya Lahadi har zuwa ranar Litinin.

…………………………………..

Your Comment

You are replying to: .
captcha